AWARAN kwai.....KUYI subcribe domin samun cikakkun girke girke

AWARAN kwai
Abubuwan hadawa

Kwai
Attarugu
Albasa
Man girki
Maggi
Leda
Yanda ake hadawa

Da farko zaki sami kwanki ki fasashi a kwanan ki mai kyau ki kadashi
Sai ki zuba kayan hadinki: attarugu, da albasa wanda dama kin yi giretin nasu da sauran kayan dandano dai dai misali
Sai ki dunga zuba kwan naki acikin leda kina yi  masa kamar kullin alalan leda
Sannan sai ki dora ruwanki cikin tukunya ki dafa kullallen kwan naki
Idan ya dahu sai ki kara fasa wani kwai, kuma ki cire wannan kwan naki na leda kina yankashi yankan tsakiya za kiga ya bada shef  din zuciya, watau ‘heart’ sai ki dunga tsomashi acikin wannan kwan naki
Sai kuma ki soyashi a manki mai zafi sosai, amma ki yi suyar sama-sama don ya yi suya mai kyau.....
Aci lafiya kiyi share da SUBCRIBRE

Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYA💘💘

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..