Posts

Showing posts from October, 2018

A jininshi ne

Ajininsa yake 1-01 Posted by ANaM Dorayi on 07:24 AM, 03-Nov-15 Under: Ajininsa yake __________________ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ ________ Rabe jikin daya daga cikin bishiyon da suka yi wa filin sukuwar kawanya. Jikinsa kayan mkrntar firamare ne. Farar riga da koren wando. Gaba- daya hankalinsa tattare ya dora bisa dawakan da ke zuba tsere kamar za su tashi sama. Babu abinda yake tunani, illa ina ma shine bisan dokin da yayi wa saura fintankau?" Jama'a suka hau ihu, don taya mai dokin daya zo na farko murna. Shi ma ya kwasa a guje. Yana isowa bai ma san ya jefar da jakar littattafan sa ba. Ana ture shi, yana turawa, sai da ya kutsa ya ta6a jikin saurayin daya zo na farko. Kamar an sanya shi al-janna, haka yake ji cikin ran sa. Wasu rukunin dawakan ne za su taso yanzu, shi yasa duk jama'a suka koma inda suke. Haka shima ya nemi wata bishiyar ya kuma ra6ewa jikin sa na tsuma, tamkar na 'yan dambe. Caraf! Ya ji an cafke kunnunwan sa 2, a fir...