[14/01 10:15 am] Ummu Basheer: 🌹 *A KAN K'ANWA TA* 🌹 🌹 { *LOVE STORY* } *NA* *UMMU BASHEER* *PAGE* *1*~*2* *Gudu* take yi sosai fatan ta d'aya ta isa gida, da alama daga makaranta take, Dan Uniform ne a jikin ta, shiga gidan tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri ta d'auki buta ta shiga bayi. Wata datijuwa ce ta fito daga wani k'aramin Kitchen tana cewa"Yanzu haka y'ar banzan yarinyan nan ce ta shigo da gudu, kamar...." Maganar ta ne ya katse lokacin da taga ta fito. Kallon ta tayi tace" *DEEJA* Allah ya shirye ki, dama nasan kece zaki shigo haka" Yarinyan da aka Kira DEEJA ta rik'e k'ugu tace" Ameen shiriya ta addinin musulunci" tayi fari da ido. Tsaki tsohuwar taja tace" idan kin gama rangwad'a sai ki wuce ki d'auki abinci kici" DEEJA tace"Cab ai Ina yanzu gidan su lantana z...
Comments
Post a Comment