AKAN KANWATA👫

[14/01 10:15 am] Ummu Basheer: 🌹 *A KAN K'ANWA TA* 🌹

                   🌹

     { *LOVE STORY* }



   *NA*

*UMMU BASHEER*

     
 *PAGE* *1*~*2*




 *Gudu* take yi sosai fatan ta d'aya ta isa gida, da alama daga makaranta take, Dan Uniform ne a jikin ta, shiga gidan tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri ta d'auki buta ta shiga bayi.


 Wata datijuwa ce ta fito daga wani k'aramin Kitchen tana cewa"Yanzu haka y'ar banzan yarinyan nan ce ta shigo da gudu, kamar...." Maganar ta ne ya katse lokacin da taga ta fito.

 Kallon ta tayi tace" *DEEJA* Allah ya shirye ki, dama nasan kece zaki shigo haka"

 Yarinyan da aka Kira DEEJA ta rik'e k'ugu  tace" Ameen shiriya ta addinin musulunci" tayi fari da ido.


 Tsaki tsohuwar taja tace" idan kin gama rangwad'a sai ki wuce ki d'auki abinci kici"

 DEEJA tace"Cab ai Ina yanzu gidan su lantana zanje, tayi gulma na inji mairo dan haka dole inje inyi maganin ta"


 Tsohuwar tace" Kai wannan yarinya akwai jaraban tsiya, wuce ki cire kayan makarantar tukuna"


 Tsaki tayi take" ke fa *INNA* kin cika takura" tana fad'in hakan tayi waje da gudu, Dan dama fitsari ne ya matse ta shiyasa ta dawo gidan.

 Sallati INNA tayi tana cewa"Allah ya shirye ki DEEJA"Gidan su lantana DEEJA ta nufa tana zuwa ta aike wani yaro ya Kira ta, Lantana na fitowa DEEJA ta cakumi wuyan rigar ta tace" Wa na kama, magulmaciya kawai, to Mairo ta fad'a min gulma na da kukayi"

Zaro ido Lantana tayi tana had'iye yawu da k'yar ta hau rantsuwa akan ba ita bace Dan tasan halin DEEJA, yanzu sai tayi mata duka, gashi ita ba k'arfi.

Tsaki DEEJA tayi tace"ki bar wani rantsuwa ne yarinya yau sai kin gane kuren ki" ai Nan ta hau kokuwa da Lantana, sai dambe suke, Lantana da taji a zaba sai ta fara kuka tana ba DEEJA hak'uri, amma Ina ko sauraran ta Bata yi ba, can sai ga wani mutum ya zo wucewa, Nan ya daka musu tsawa amma DEEJA bata bari ba, sai da yayi magana yace" Kai kun ci gidan ku ba magana nake muku ba?"

Rik'e k'ugu tayi tace"yo ai ita ce ta fara tsokana ta"ta murgud'a Baki.

Ganin DEEJA ce yasa mutumin wucewa ba tare da yace komai ba, tsaki taja tace"Shigigi plus gad'are = bitazaizai, ko Ina ruwan shi da mu" juyawan da zatayi sai taga ashe Lantana ta shige gida da gudu, tsaki taja irin zamu had'u d'in nan.


Gida ta koma tana zuwa ta tarar da INNA tana daka, samun guri tayi ta fara murza ido cikin fuskar tausayi tace" INNA yunwa nake ji, Zan mutu"😔

 Hararan ta tayi tace"to sai ki mutu in gani"

Kuka ta rushe da shi da k'arfi ta fara cewa"wayyo Zan mutu, jama'a INNA zata kashe ni"

 D'aukar mafici INNA tayi ta jefa mata tace" rufe min baki ja'ira"

Da k'arfi tace"wayyo yunwa, *YAYA NA* zan mutu kazo ka cece ni"

Mik'ewa tsaye INNA tayi tace" Yi shiru in d'auko miki kar ki Kira min Yayan Nan naki"


 Da sauri ta mik'a mata abincin, karb'a tayi ta fara ci, can tace"Kai INNA ta kin iya girki fa sosai, sai dai kin cika massifa"

 A fusace tace" Uwa ki ce mai massifar, kiyi min shiru kar ki ishe ni tohm"

 Dai-dai lokacin ne wani Kyakyawan saurayi, fari ne amma ba sosai ba ya shigo gidan, DEEJA na ganin shi ta mik'e tsaye da sauri ta Isa gurin shi tana cewa"oyoyo YAYA NA"

 Murmushi yayi cike da k'aunar k'anwar ta shi yace"oyoyo *K'ANWA TA*, mene ne ya same ki naga idon ki ya canza?"

 Juyawa tayi ta kalle INNA tare da nuna ta da hannu cikin shagwab'a tace"ga ta Nan wannan INNA, sai da taga dama ta bani abinci" ta murgud'a Baki.

Rik'o hannun ta yayi suka zauna kan tabarma yana cewa"INNA ki bar min *K'ANWA TA* ta huta please"

 Da sauri DEEJA tace"to kin dai ji koh tsohuwa?"

Dariya INNA tayi tace"naji naji 'yan mata Kuma takwara ta HADIZA"

B'ata fuska tayi tace"YAYA NA kaji ta ko wai nice HADIZA" ta fara kukan shagwab'a.

Da sauri ya fara lalashin ta yana cewa"A'a ba haka sunan ki yake ba, INNA ki gyara kinji INNA?"cikin lalashi.

Murmushi INNA tayi tace" Kai Dan Allah k'yale ni haka, yo idan ba sunan ta bane sunan wace ce haka?" Tashi tayi ta shige Kitchen Dan kawo mai abinci.


 Fito da wani leda yayi na tsire ya mik'a ma DEEJA, karb'a tayi tace"YAYA NA Allah ya k'ara bud'i"

Yace"Ameen K'ANWA TA"


 INNA na zuwa ya mik'a mata nata, Nan tayi godiya, aiko ya tasa DEEJA a gaba yace ai dole sai sunci abincin tare duk da taci nata sai da suka ci tare course kusan kullum tare suke cin abinci.
hegari da safe

 DEEJA na gani anci uban kwaliyya irin na 'yan k'auyen Nan duk anyi d'ige-d'ige a fuska, d'an k'aramin bakin nan nata yasha jambaki har ta gefe, sai wani rangwad'a takeyi a dole irin ta had'u d'in nan sosai, kayan makaranta tasa ta fito.

INNA dake dama Koko ta gan ta, tab'e baki tayi tace" oh ni HADIZATU irin wannan kwaliyya haka, Allah ya kyauta"

 Turo baki gaba tayi tace"yo Wai ni Ina ruwan ki da kwaliyya ta ne dad'in abin ma nafi ki kyau"😏

Tuntsirewa da dariya INNA tayi tace"waya yaga gwagwan biri"

Ihu DEEJA tayi tace"wayyo ni YAYA NA"

 Da Sauri YAYA ya fito daga wani d'aki da alama ma barci yakeyi, Yana zuwa ya hau tambayar meya faru,

Cikin shagwab'a tace"ba ga tanan ba wai nice gwagwan biri"

Zaro ido yayi😳 yace"Haba INNA yanzu K'ANWAR tawa ce kike Kira haka, ke ko gajiya ba Kya yi da sasafen nan Zaki sa min ita kuka?"

Tsaki INNA tayi tace"na sa tan kasan Allah *BILAL* ka fita ido na, na gaji da irin abin da ke faruwa akan yarinyan nan, kullum cikin sa mutane magana take kullum a k'auyen Nan sai ta janyo mana magana bata da aikin yi sai tsokanan Yara, manyan ma bata k'yale su ba, Kai Kuma ka hau ka zauna kan maganar ta, to ba zai yuwu ba a toh"

Kallon K'ANWAR shi yayi yace"kinji na YAYAN ta zo ki karya ki tafi makaranta karki kula maganar INNA da kullum ba ya k'arewa"

Cikin shagwab'a tace"ni gaskiya YAYA NA bazan Sha Koko ba, shayi da biredi Zan Sha"

Da sauri yace"oya shigo d'aki na in had'a miki, INNA akwai ruwan zafi?"

Cikin takaici tace"sai dai ka d'aura, 'yan gayu masu Shan shayi, Koko dai yafi lafiya in gaya miki yarinya"

 D'akin BILAL suka nufa DEEJA ta juyo tace" eh na dai ji bazan Sha Kokon ba ehe"😏


 Nan ko Yayan ta ya had'a mata tea and bread mai kauri tasha sannan ta wuce makaranta, duk k'awayen ta sai da ta fad'a musu tea and bread ta karya da shi, haka akayi karatun shima sai tsokanan y'an aji take ana tashi ta gudu dan kar su kama ta su jibga😂.


 A can wani lungu ta tsaya ta jira su Mairo, suna zuwa duk suka tuntsire da dariya, d'aure fuska tayi ai Nan sukayi shiru cikin Jin tsoron ta, Nan tace" yau gonar malam Audu za muje mu samo mangwaro da gwaiba"

Nan dukan su, su ukun sukace"Angama ranki shi dad'e"
 Mairo, Lantana da Hansai sune k'awayen ta, Nan suka nufa gonar ai ko sunci sa'a ba kowa Nan suka shiga gonan suka hau bishiya suna tsinkowa amma fa DEEJA bata hau ba dan ita bata hawa bishiya sai dai tasa su hau Dan shegen tsoro ne da ita, suna saukowa kamar daga sama sai ga malam Audu da gudu ya biyo su, ai Nan suka ruga da gudu suna tsere, shi ko cewa yake"yau Naga mayun Yara masu kama da aljanu ke Kam DEEJA garejin Yayan ki zanje sai ya biya ni" ganin sunyi Mai nisa shi Kuma baya iya gudu sosai sai ya hak'ura akan zai je gurin Yayan ta dan ita ce shugabar su Mairo.


  Dai-dai wani lungu suka tsaya ganin ya daina bin su, da kan ta DEEJA ta karb'a mangwaro da gwaiban ta raba musu amma nata duk yafi yawa, duk da sun san bata kyauta ba haka nan sukayi hak'uri saboda sanin halin ta, sai a wannan lokacin ne kowa ta nufa gidan su.


 DEEJA na shiga gida taga ba kowa a tsakar gida sai ta fara yin a hankali kar INNA ta ji shigowan ta, aiko zata shiga d'akin kenan INNA ta fito bayi tana cewa"sarkin yawo sai yanzu?"

 Juyowa tayi tace"tun d'azu na shigo fa kina bayi Killa Kashi kike Dan na jima"☹

"Ke dalla rufe min baki, uwar ki ce ke kashin, y'ar banzan yarinyan kawai, ni wuce ki bani guri kin tsare ni da ido"

 Juyawa tayi ta shige d'aki tace"oho dai gaskiya na fad'a"🤷🏻‍♀





Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYA💘💘

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..