AURAN MANUFA 3-0,3-2

[04/11 11:33] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣0⃣ Cikin dare yau ma na farka na ganshi yana tilawar karatun alkur'ani irin na jiya sai wajan asuba naga ya idar da karatun yana bisa kujera waya naji yana yi amma maganar kasa kasa zuciya duk wanda ya bi mata sai ta kaishi ta baro shi saboda sai zuciyata ta mini kila da Fa'izansa yake waya, tun da sam bana jin abinda yake fada. Kuka na shiga yi daga kwancen amma ban bari sautinsa ya bayyana ba don kada ya san shi nake wa kuka. Dole inyi kuka saboda wannan wulakanci ne na karshe ace kana kwance da matarka ta aure cikin daki daya amma ka kwana kana hirar soyayya da wata. Ni nasan bai san ido na biyu ba da ya tsinke hirar tasu. Da na gaji da ganin wayar da yake yi bansan me yake fada ba sai nayi alamun da zai zaci ko zan farka so nake hirar ta kare saboda juriyata ta kusa karewa (Allah sarki rashin sani) motsi na yi bisa gadon nayi juyi na gyara kwanciya duk da dakin babu haske so sai amma ina kallonsa motsina sai yasa bi gadon da kallon amma bai daina wayar ba hakan ma ya isa yasa in gane bada mace yake waya ba tunda da mace ce da yaga haka da sai ya kashi wayar amma ni ban gane ba sai ma na dada kuluwa ni a dole ya wulakanta ne ya tozarta ni. [04/11 11:34] ‪
4/11 11:34] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣1⃣ Da asuba da ya tashe ne inyi sallah sai yaga idona a kumbure sunyi ja sai yasha jinin jikinsa ya tambaye ne, me ya sami idonki? Ko baki sami yin bacci ne idanun ki suka kumbura? nace, nayi bacci ashashshe kafin dai in kwanta ne wani abu ya fada mini a ido na dauka idan nayi bacci na tashe zai da yi min zafi sheni suka kumbura saboda na murzasu. Zuwa anjima idan basu daina zafi ba sai muje asibiti je kiyi sallah bari inje masalaci. Harara na bi bayansa da shi saida ya fice sannan naja tsaki nace, dube shi don Allah kamar wanda ya damu dani, Alhalin shi ya haddasawa idanuna kumbura. Dana koma daki ma tambayoyi hajja ta rufe ni dasu itama amsa iri daya da wadda naba Ya Faruk na gaya mata. Nayi wanka ina zaune da dan tawul iya rabin cinyoyi ina shafa mai sai kawai naji sallah mar mutun ban ankara ba na ya shigo duk saina daburce gashi hajja bata dakin tafi ta sa turan wuta a falon nasan ya ganta shi yasa baijira an amsa masa salama ba ya shigo. Jikina rawa yayi na yayamo zani na daura ina lura dashi yadda yabi cinyoyi na da kallo, amma da ya ga mun hada ido sai yayi saurin dauki kansa shi a dole bisa tsautsayi ya kalleni. Na dauki wani karamin hijabi nasa saida na gama kidi mata sannan ya dube ne yace, da ma zan dan fita ne shine nace bari in gani idan idon bai daina ciwo ba saimu wuce asibitin. Nace, na wanke shi da ruwan dumi da gishire ya daina ciwo. Yace okey to Allah ya sawake ni zan fita amma yanzu zan dawo. Nace, to a dawo lafiya. Fita zaiyi baki yi masa abin karyawa ba? nace, fita zaiyi amma yace ba zai dade ba yanzu zai dawo. Tace, sai ki kokarta ki shiga kicin kiyi masa abinda zai ci kin girki sai yana saye zuciyar miji bale ida mace ta iya nau'o'in girki sai kiga duk inda yaje sai ya dawo yaci abincinta in tafiyar kwanace ta kamashi da kyar zaki ga yana iya cin abincin otal sai ki bada himma wajen iya girki da tsaf tace shi don na lura mijinki sarkin tsaftani dan gayu. Ni dai ban yiwa hajja musu ba amma nasan ko nayi girkii da wuya wannan sarkin iya yin zaici tunda tun asali baya cin abu
4/11 11:34] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣2⃣ Asali ma baya cin abu idan muka yi amma ban san yanzu ba nayi shirina tsaf kamar zani wata shahararriyar unguwa sannan na nufi kicin din don in game ya kamata inyi masa stord din da aka shake mana da kayan abinci na bude na duba na ga kayan abinci ne shakare ni ban ma san yadda zamu yida suba sai dai rabawa dangi. Na farke buhun fulawa na debi kadan dai dai yadda zata ishemu na debo kwai wadatace sannan na dawo kicin din (meat puffs) zanyi mana na zuba filawar a cikin wata container ta silver sannan na fasa kwan akai nayi ta bugawa sannan na zuba ruwa na cigaba da bugawa dama tun shiga ta kicin din na wanke nama na dora a wuta saina duba naga ya dahu saina sauke na kwashe shi na dauko abin nika nama na nika shi sai na juye a cikin bugaggiyar fulawa da kwai din nan na nika albasa da atarugu sannan na zuba a ciki sai nasa curry tyme da magi sai gishiri kadan sai nayi ta cakudawa ya hadu so sai sannan na dora mai a wuta na fara soyawa nan da nan gidan ya dau kamshi. Ina tunanin Ya Faruk ya kusa dawowa shi yasa sai na dama masa koko na zuba a wani jug mai rike zafi saboda su Ifty sun gaya mini yawanci abin karyarmansa kenan. Naje na shirya dinning table din mu tsaf na goge ko ina sai kyalli yake yi abin kaga gilas nayi haka ne don kada sarkin tsaftar yaga gurin da kura. Na dauki namu na wuce dakina dashi. Hajja santi ta dinga zubawa wai wannan abunda na soya soyen zan dinga yi zan kwace mata miji. Muna cikin dariya sai gashi ya dawo ya dan leko yayiwa hajja sannu ya fita. Ta dube ne tace, tashi ki bishi ki bashi abincin nasa, kullun ana koyawa mutum abu bazai dauka ba. Lafiya na dauka na nade jikina zan fita tace, bana ce idan zaki gurin mijinki daina nade jikiba? Shifa ya halasta yaga komai naki. Nace idan naje dakinsa ina cirewa amma yanzu kinga kayan jikina sun matseni zaki iya ganin muna zaune a falon yayi baki maza shi yasa nake rufe jikina shima yace gara in dinga yin haka. Kaji karya yau shema ya bita kan lamarina balle ya san me nake yi'ni dai ina yin haka saboda bana son ya ga

Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYA💘💘

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..