AURAN MANUFA 3-3,3-4

[04/11 11:35] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣3⃣ Kaji karya yau shema ya bita kan lamarina balle ya san me nake yi ni dai ina yin haka saboda bana son ya ga kamar don inja hankalin sa nake sa matsatsun kaya shi yasa nake boye jikina. Ina fita na ganshi a falo ya harde a doguwar kujera (3 seater) da mutuniyar tasa yana sana'ar wato (daily trust) ita yake karantawa ina jin ma ita ya fita sayowa. Na matsa daf da shi nace, ga abin (break fast) dinka can bisa (dinning) ya dube ni yace, I am sorry ina azumi ai ban san zaki yi ba dana gaya miki da baki wahalda kan ki ba. Raina ya sosu haka kurum hajja ta sani sai cusa kai nake yi gurin mutum amma shi sai gwalene yaki yi ya zanyi bari dai hajjan ta gama kwana bakwanta ta tafi idan yace haka zai cigaba dayi mini to bazan jure ba yana yin zamanmu zai canza zan kama kaina kuma ni na san ba wani azumin da yakeyi in ma yana yi to don kada yaci abinci nane ya tsiri azumin. Na daure nace, shike nan dare me za'ayi maka na buda baki? Yace kada ki damu bana cin abinci mai nauyi da dare tea kawai zan sha. Nayi jima rama nace lallai wannan mutumin dani yake zance wato har yanzu yana tunanin ban gama kaiwa matsayin da zanyi abinci yaci ba kenan shike nan nasan yadda zanyi muje zuwa. Na juya abina na koma daki hajja tace, har ya kamala cin abincin? wai azumi yake, tace, ai ya wuce wai zai yi miki karya ne? nace, ba wani azumin da yake yi kin san shi sarkin tsafta kila gani yake ban iya girki ba ko bani da tsatfa tunda haka yake mana a gidansu idan mamata samu yin girki in dai ya san shi mu muka yi baya ci ni ina ruwa na cikin sa ya cuta. Hajja ta rufeni da fada waidon me zance haka bayan ta gama fadan kuma ta koma yi mini nasiha.
/11 11:35] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣4⃣ Daren yau da yake na san abinda na shirya shi yasa da nayi wanka nayi shirin baccina banjira tace in tafi ba nayi mata saida safe na fice inaji tana cewa, ko kefa ashe dai kin san abin da ya kamata dama shakiyanci ne. Ni kam nasha alwashin insha Allahu na bar kara zuwa dakinsa kwana don bazan iya jurar wulakanci tunda ai bashi da lokacina daga sallah sai karatun qur'ani yake yi maimakon idan ya gama ya nuna kullawarsa a gare ne a'a gara yakarasa daren da yin waya shi yasa zan barshi koma da wace ce wayar gara in barsu inbai gani baya saki jikinsa su soye da kyau. Dakunan da aka gyara na saukan baki na shige gadon gyararre babu abinda babu saina kashe fitila mai haske na kunna bacci nayi addu'o'ina sannan nayi kwanciyata lakadan ba fargabar komai, bacci nayi mai isata saboda ko sallar nafila da ya kamata in tashi inyi Allah bai bani ikon farkawa ba, a dalilin duk dare bana samin yin bacci da rana kuma baki ba shakatawa sai dare yayi shi yasa har na so in makara don sai biyar da rabi na tashi.

Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYA💘💘

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..