AURAN MANUFA 3-5,3-6

04/11 11:35] ‪+2347033360730‬: AUREN MANUFA 3⃣5⃣ Ina dar da salla a dakin da na kwana sai na baro dakin don kada Ya Faruk ya dawo masallaci ya leka can dakina yaga bai ganni ba kada kuma ya tambaye ni labari yasha bam bam da kuwa na shiga uku da fadan hajja kila ma tace sai ta gayawa mome ko dadi ni kuma tsorona Allah tsorona laifin da za'aje ace musu muyi wa mijina kada suga ba'aje ko ina ba na fara ruguza biyayyar da na basu tabbacin nayi musu, koda abubuwa zasu canza yadda na lura da take takensa shima yafi son sai hajja ta bar gidanmu nima nafison kada muyi komai da zata fahimci zamanmu na yan marina ne. Ina shiga dakin na isketa bisa sallaya bance mata komai ba kawai saina warware lafayar jikina na haye gado na shige cikin bargo ba bacci zanyi ba amma dai ina so in kwanta ne kawai. Ban dade da kwanciya ba hajja ta tashi daga abin sallar ta koma bisa kujera ta zauna na yaye bargo nazo na gaisheta ina shirin mikewa inje in sake kwanciya saiga wanda nake tsoron kada ya shigo dakin ganni da matsatsunriga da wando yayi sallama ya shigo dakin baccin nawa da sauri na koma nayi zaman cin tuwo a gaban hajja kallo daya yayi mini yayi saurin maida ganinsa gurin hajja yana gaisheta suna gama gaisawa nima na gaisheshi ya wani kasheni da idanu yana kare mini kallo banda matsatstsun kayan dake jikina ma kaina babu kallabi ga kana nan kitso na sun watsu a gadon bayana babu inda idanunsa basu karade da kallo a jikina ba ni kuma duk saina muzanta inaso in tashi amma kafafuna sun gaza motsi dole na hakura na zauna. Ya tsaida idanunsa cikin nawa yace, yaya kika kwana da idon naga yau basu yi ja ba? Gabana ya fadi Allah yasa kada ya tona mini asiri ya nuna cewa ban kwana a gurinshi ba. Nayi saurin cewa, sunyi sauki. [04/11 11:36] ‪+2347033360730‬: AUREN MANUFA 3⃣6⃣ a takaice don bana son inja maganar da tsawo. Ya mike yace wa hajja, zanje in kwanta saina fito zuwa anjima. A raina nace, ai dole kaje ka kwanta kayi ramuwar bacci tunda an kwana ana waya da masoyiyya. Kamar yaji abinda nace sai naga ya dan kalleni yana wani miskilin murmushi. Bayansa nabi kamar yadda hajja tace inje inji me yake sona karin kumallo dan wulakancin nawa yau ma sai yace mini yana azumi saboda bakin cikin gwalene da yake yiko gayawa hajja abinda yace banyi ba kawai saina haye gado na kwanta sai ta tambayeni bazaki shiga kicin din bane kika kwanta? nace yace yau ma yana azumi kowa zai nuna ma walittaka da takawa oho? inaji hajja tana nanatawa "azumi". Allah ya bada lada. Ita naga ta soma zargin wani abu tunda naga damuwa karara a fuskarta. Ta tambaye ni, ba a gurinsa kika kwana bane naji yana tambayarki ya kika kwana da ido? na yi saurin cewa, can na kwana ina idar da sallah da naga bai dawo masalaci ba shine na taho daki. Tace nifa da kika ganni nan zaune ba zaman haka kawai nake bana zauna ne don in saki a hanya in kwaba miki idan kinyi ba dai dai ba bana son bayan na bar gidan nan mijinki ya kawo karar kinyi masa wani abu badai dai ba shi yasa tun yanzu nake sonki tafi yarda komanki cikin tsarin addini kiyi abinda zaki faranta ran mijinki ki tsaya masa arai kamar kafumar kusa a bango daga yanzu bana sonki baro gurinsa da wuri har sai inshi ne yace ki taho kuma da yace baya cin abu mai nauyi da dare ba zai yiwu ke ki kyale shi yayi azumi yayi buda baki da zallan ruwan tea ba yau ki shiga kicin ki hada masa duk wani abu da kika sani mara nauyi, kada ki kara kyaleshi ya dawwama da shan tea. Bin hajja nayi da to saboda na san duk yadda na fahimtar da ita mijina murdadde ne ba zata gane ba tunda nariga nasan halinsa tun kafin muyi aure yana da wuyar a canza masa ra'ayi.

Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYA💘💘

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..