AURAN MANUFA 3-7,3-8

11 11:36] ‪+2347033360730‬: AUREN MANUFA 3⃣7⃣ Bai dawo gida ba tunda ya fita bayan la'asar sai ana kiran sallar magriba muka ji hon motarsa hajja ta dubeni tace, ga mijinki can sai ki shiga kicin ki dauki abun sha mai sanyi ki tare shida shi, idan ya dawo sallah sai ki gabatar masa da abubuwan da kika tanadar masa ki zaunar dashi cikin hira da kissa ki nuna ko dan yaya ne yaci da yawa indai girkin yayi dadi maza tashi kije. Na shiga kicin na dauki madarar holandia mai sanyi sai juice 5 a live na hada sannan na nufi dakinsa harya dauro alwala ya fito zai je masallaci ya tareni ya amshi kayan hannuna yace, masallaci zanje bani holandian din da na zuba nace, zanje inyi sallah ne. yace jiya me ya hana ki zuwa taya ne kwana? idan nazo me zanyi maka bayan kana da me taya ka debe kewa a waya. A zucci na fadi haka amma sai a fili na ce, baccine ya dauke ni ban sani ba shi yasa. Yace, to yau kizo. Ya mika mini kufin cikin sauri ya wuce massalaci ni ma barin dakin nayi na koma nawa dakin. Allah yasa ban zuba abinda hajja ta matsa inyi masa ba saboda na san bazai ci ba sai dai aba almajirai shi yasa na shirya kuloli babu komai a ciki bisa dinning don kada hajja tace ban bi umarninta ba ai kuwada nace ga abincinsa can sai cewa yayi inyi hakuri tea kawai zaisha ban nuna masa naji haushi ba amma yadda ya bukaci inzo taya shi kwana sai na fanshe haushi na anan naki zuwa dakina na jiya can na kwana ma yau. Ranar hajja zata tafi ranar kwananta na bakwai tun safe nake mata kuka nace ni dai bazata tafi ba inba haka ba idan ta tafi nima zan biyota gidan. Ta dinga lallashi na tamkar yarinyar goye, kina da hankali ne zaki ce biyo ni haba Hanifa ya zaki tada hankalinki dubi yadda yaron nan yake nan nan dake indai yana gida aikinsa kenan ya leko yaga ya kike kulawa dai dai gwargwado yana yi miki to me kika rasa?. Kiyi hakuri idan an kwana biyu zanzo in sake duba ku sannan baga waya basai mu dinga magana duk abinda ya shige miki duhu idan baki kirani a waya ki tambayeni ni kawarki ce. [04/11 11:37] ‪+234 810 272 5985‬: AUREN MANUFA 3⃣8⃣ 25: Ko kin daina kawancen dani? dole nayi dariya hajjama tayi dariya tace, yauwa haka nake so" Faruk ne da kansa kai hajja acan ya iske Ya Saif suka fito tare da yake Ya Saif bai koma ba hutun karshen shekara yazo. Suna hanyar zuwa gidanmu ne Ya Saif ya watsowa Ya Faruk tambayar da ta kwana bakwai tana kwakular wadda ada ya kanne bazai yi taba amma yanzu kalaman da yaji hajja na fada na yadda su Faruk da matarsa ke zaune lafiya a dalilin bin umarnin iyayensu da suka yi sai ya tsinke ya tuno ranar da aka zo aka ce wai Hanifa ta kai budurcinta yaga ana ta murna da dafe dafen abinci to wai ko aminina sa ya karya alkawarin daya daukar masa ne ya canza MANUFAR Aurensa da Hanifan. Damuwa karara ta bayyana a fuskarsa ya daure yace, Friend ko ka san tun kwana bakwai da suka wuce da aka cewa wai Hanifa ta kai budurcenta naga ana ta shagula fargaba ta dameni ina tunanin ko ka kasa rike alkawarin da kayi mini ne? dariya Faruk yayi ya dan dubi Saif sannan ya maida hankalinsa gurin tukin da yake yi yace Deen kenan kana tunanin zan iya karya alkawarin dana daukarwa nagartacen amini kamar ka? Gaskiya banyi tunanin zaka kawo faruwar hakan da gaske a zuciyarka ba kana son in rantse maka sannan kayar da dani? Saif yayi saurin girgiza kai yace, wallahi na yarda da kai babu haufi a aminta karmu amma (how comes) ka shirya (plan) din faruwar hakan gaskiya kashigar da iyayen mu so sai.

Comments

Popular posts from this blog

AZABTACCIYAR SOYAYYA💘💘

AUREN MANUFA 2-4

AUREN MANUFA 2-7 ZUWA 2-9..