AURAN MANUFA 3-9,4-0
11 11:38] +2347033360730: AUREN MANUFA 3⃣9⃣ Faruk yayi murmushi, ya gaya masa yadda yayi ya shirya hakan tare da goyan bayan Hafina suka shirya komai ya kara da cewa itama na lura taji dadi da nayi haka don har yanzu na lura bani a gabanta balle taji haushi banbata hakinta ba haba ni wannan yarinyar ai tayi mini kadan duk ranar da naje mata da bukata ai ina sai buzunta don zata ji jiki sam ma ba zata iyada lafiyyaye kamar ne ba yadda take yar lange lange koda yake tana da fadi ta kasanta amma ina she is too young nafi karfinta bazata iya dauketa ba. Dariya sosai Saif yayi yace, ashe Allah ya taimaki yar kanwata data gane kurinta nine nan fansarta kana nan kana azumin da nasan kana yi na kare kai daga sha'awa? yace inayi babu fashi amma kasan sarai daci ance sheyaki kawo jin yinwa ko? To ni ban danganta bukatata a tare da ita ba inda nakai tawa daban shi yasa ko jikina ban damuba koda a bargo daya zamu kwana. Ya Saif dai shiru yayi amma abin nasa shi cikin kokwanto saboda bakowane lafiyyen namiji bane zai iya abin da Faruk ya fada saboda Hanifa tana da abubuwa masu daukar hankalin da namiji inba wanda yakai zuciyarsa nesa ba gaskiya babu wanda zai iya kauda idonsa a kanta balle shi Faruk da yake mijinta take matsayin matarsa mallakinsa halak malak anya zai iya boye sha'awarsa a kanta? Saurin kawar da hakan Ya Saif yayi a zuciyarsa don baya fatan abinda zuciyarsa take yawan ayyana masa ya zamo gaskiya wata rana sun iso gidanmu suka tarar gidan tsit bana babban falonmu Faruk ya haye dakinsa na sama bai dade baya fito ya iske Saif ya tasa T.V. agaba labaran CNN yake kalla har Faruk ya zauna sai ya dube shi yace, na san tana can dakinta tana bacci don na lura sarkin bacci ce. [04/11 11:38] +234 810 272 5985: AUREN MANUFA 4⃣0⃣ Ba da san ransa ya nufo dakina ba saboda yanzu tunda hajja ta shige idan mun hadu a falo shike nan ma tambayi lafiyar juna idan kuma bamu hadu ba to a sauka lafiya don baya son abin da zai sa ya zubda girman sa a guri nashi yasa ya sha alwashin jan ajiosa. (kunjifa jama'a mijine zai jawa matarsa aji) Bana falo na can kudune bisa gado ina aikin kuka sai kira'ar Jabir dake tashi adakin don kukan da nake ba mai sauti bane hawaye ne zalla ina kokawa kaina ne shin wace irin rayuwa zan fuskanta yanzu a gidan nan da ba hajja? Wulakanci ne daina san sun shirya dakonsa kwando kwando tunda koda hajja tana nan aboye Faruk yake mini gashin kuma yana gasa mini gyada a tafin hannu a gaban hajja ne yake nuna kulawarsa a kaina tunda ko abincinda take da ina dafa masa tsawon kwana bakwai bai taba ci ba kosau daya itace dai take ganin kamar yana ci wannan ma kadai wani nau'in wulakanci ne ka dafa domin mijinka amma yace baya ci. Kaina yazo ya tsaya ya kira sunana na dago ido na da suka yi ja na amsa, na'am. Yace ai har yanzu kukan kike ye? Lallai aiki ya ganki. Ki taso ku gaisa da Deen. Na kwantar da kaina nace, ba zan iya zuwa ba jiri nake ji ka gaishe shi. Ko sannu baice mini ba ya juya ya fice abinsa wannan halin ko in kula daya nuna mini ya kara tunzira zuciya ta lallai yanzu ne zan tabbatar da an kawo ni gidan mijin da baya sona yanzu ne zan soma zaman hakuri da zaman hadiyar duk wani nau'in wulakanci da zai yi mini. Yunwa Ya Saif yake ji lokacin shi ya sa da Faruk ya koma yace masa ina bacci sai yace ya bashi abinci dana na dafa yaci ya dube shi yace, Kaima ka san bana cin girkin yara ka shiga kicin din ka duba kila ka sami wani abu. Saif ya tashi da saurin sa ya nufi kicin din saboda yayi kewar cin girkina mai dadi fiye da na matarsa shi idan da halima kullum nan zai dinga zuwa yana cin abinci na tunda shi aminin nasa ba yaci. Ya duba cikin wata warmer ya iske nayi (cream macaroni cheese) sai turiri take yi ga dadin kamshi na tashi dana dafa naci ne yayi mini yawa shi ne na ajiye.
Comments
Post a Comment