DANBUN SHINKAFA DA KARAS..AYI SUBCRIBE
BUBAWAN DA AKE BUKATA.
1= Shinkafa
2= Karas
3= Koren wake
4= kabeji
5= albasa
6= attaruhu
7= Sinadarin dandano
8= gishiri
9= hanta
10= man gyada
YADDA AKE HADAWA...
Da farko dai za ki samu shinkafarki iya adadin da ki ke bukata, ki kai a barzo miki. Ki fidda garin ta hanyar tankadewa ki dauki tsakin ki wanke shi tas! Ki zuba amadanbaci, ki rufe ruf da leda sannan ki daura a wuta ki kawo murfi ki rufe dan ba’aso tiririn ya dinga fita. Ki tabbatar kin zuba ruwa a kasan tukunyar daidai yadda ba zai kone ba.
Ki tafasa karas dinki sama-sama. Ba lugub ba ki yayyanka shi bayan kin kankare bayan. Shima koren wakenki tafasa shi, akwai wanda ake siyarwa bararre kuma busasshe to da shi za ki amfani. Kabejin ma ki wanke shi tas ki yanka amma ba kanana can ba.
Attaruhu da albasa ki yankasu su ma yadda ki ke bukata. Ana so albasar ta yi yawa. Hantarki k itafasa da isasshen sinadarin dandano da dan gishiri, ki yanka gutsi-gutsi. Bayan tsakinki ya yi laushi sai ki sauke ki zuba mai ya kama shi, sannan ki kawo kayan lambun nan ki zuba, ki cakuda su yadda za su hade jikinsu da tsakin haka ma attaruhu da albasar nan hade da yankakken hantarna nan ki hada ki sake juyawa, sannan kidan da ka sinadarin dandano da gishiri kadan yadda ba zai yi yawa ba ki cakuda, ki mayar wuta.
Ki bashi lokaci za ki ji yana fidda kamshi sosai, ki tabbatar ya yi kamshi kuma ya dahu sosai yadda ake so, ki sauke. Za a iya ci a haka, ko kuma ki yi masa miyar kayan lambu.

ACI LAFIYA KUMMA AYI SHARE da SUBCRIBE...
Comments
Post a Comment