AUREN MANUFA 2⃣4⃣ Dana lura ne ce mace kuma a kasan kasa nake shi yasa na isa gabansa nadan risina nayi masa magana dan naga alama idan banyi magana ba kila sai dai in bushe a bangon nan. Ya Faruk sannu da hutawa? ba tare da ya kalleni ba yace, aina dauka bazaki yi magana bane, koni kike jira inyi miki magana? nace, ba haka nake nufi ba kayi hakuri. Ya nuna mini kujera daga gefensa yace in zauna na zauna a darare. Singileti ce da gajeran wando ne a jikinsa shi yasa tunda da na kalleshi sau daya ban saki kallensaba narusinar da kaina kasa shi kuma yacigaba da karaunsa. Bacci nake ji, gashi kuma na gaji da zaman da nake yi, amma na rasa yadda zanyi gashi har kusan sha biyu na dare. sai da ya gama jin kai da isarsa sannan naga ya aje jaridar ya dube ni yace, idan kina jin bacci ga gado can ki shige bedroom ki kwanta yayi mini nuni da can cikin dakin baccinsa. Girgiza kai nayi nace, bana jin bacci. Yayi murmushin yace, ok to tunda bakya jin bacci ki shiga daga ciki sai kiji d...
Comments
Post a Comment