11 11:36] +2347033360730: AUREN MANUFA 3⃣7⃣ Bai dawo gida ba tunda ya fita bayan la'asar sai ana kiran sallar magriba muka ji hon motarsa hajja ta dubeni tace, ga mijinki can sai ki shiga kicin ki dauki abun sha mai sanyi ki tare shida shi, idan ya dawo sallah sai ki gabatar masa da abubuwan da kika tanadar masa ki zaunar dashi cikin hira da kissa ki nuna ko dan yaya ne yaci da yawa indai girkin yayi dadi maza tashi kije. Na shiga kicin na dauki madarar holandia mai sanyi sai juice 5 a live na hada sannan na nufi dakinsa harya dauro alwala ya fito zai je masallaci ya tareni ya amshi kayan hannuna yace, masallaci zanje bani holandian din da na zuba nace, zanje inyi sallah ne. yace jiya me ya hana ki zuwa taya ne kwana? idan nazo me zanyi maka bayan kana da me taya ka debe kewa a waya. A zucci na fadi haka amma sai a fili na ce, baccine ya dauke ni ban sani ba shi yasa. Yace, to yau kizo. Ya mika mini kufin cikin sauri ya wuce massalaci ni ma barin dakin nayi na ...